A wata sanarwa da Abdullahi Abbas ya fitar yace babu maganar masalaha a tsakanin jam'iyyun biyu ko kuma wata tattaunawa data gabata a tsakanin jam'iyyar Nnpp da Shugaban Kasa Tinubu, Abdullahi Abbas yace Shugaban kasa maisan dorewar Demukradiyya ne.
Ya kara da cewar wannan lamari bashi da toshe balle makama jita-jita ce kawai ake yadawa,
Baya-bayan nan dai a kwai wasu maganganu dake yawa na cewar Nnpp da Apc suna zaman tattaunawar sulhu domin barin Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf ya cigaba da gudanar da mulkinsa.
Sai dai wata majiya daga bangaren Nnpp itama ta musalta wannan labarin run farko, inda a wannan karo suka mayarwa da Abdullahi Abbas martani cewar babu abinda yasani akan maganar jam'iyya data shafi kasa, hasalima abdullahi abbas yana Kano, Kuma mai gidansa Abdullahi Umar Ganduje wanda yake zaman Shugaban jam'iyyar Apc na kasa shima takansa yake domin rikon kwarya yake yana kuma dab da sauna.