A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafukanta na sada zumunta, Sadiya Umar Farouq, ta ce rahotannin ba komai ba ne, face wani yunƙurin ɓata mata suna.
A ranar Litinin ne jaridar Punch da wasu shafukan sada zumunta suka wallafa rahoton da cewa EFCC na ci gaba da bincike kan badaƙalar naira biliyan 37 da aka sauya wa ma'ajiya daga lalitar gwamnatin tarayya zuwa wasu asusu-asusu guda 38 masu alaƙa da ɗan kwangila James Okwete a bankunan kasuwanci.
Jaridar ta ƙara da cewa an bankaɗo zargin halasta kuɗin haram ɗin ne a ma'aikatar harkokin jin ƙai.
Sai dai tsohuwar ministar ta ce alaƙanta ɗan kwangilar da sunanta, ƙage ne kuma kwata-kwata ba ta san mutumin da ake magana kansa ba.
A cewarta, "James Okwete bai taɓa yi min aiki ba, kuma bai taɓa wakilta ta ba, ta kowacce irin siga".
Sadiya Farouq ta ce tuni ta tuntuɓi lauyoyinta don su lalubo zaɓin da take da shi na neman kadi a kan abin da ta kira "zargin nufaƙa da aka yi mata".