A daidai lokacin da Gwamnan Jihar Kano yake tsaka da bikin kaddamar da kadojin kasa na Dan Agundi da Tal'udu sai gashi wata kotu ta dakatar da Ayyukan Gadojin.
Wata Kotun Tarayya dake zamanta a Birnin Tarayya Abuja ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano akan yunkurin ta na amfani da kudaden kananan Hukumomi dan Gabatar da aikin Gadar DanAgundi da Tal'udu a tsarin ha'daka tsakanin Jiha da Kananan Hukumomi.
Shugabannin Kananan Hukumomin Kano su 44 suka shigar da Gwamnatin kara gaban Kotu.