Rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarar kama masu aikata laifuka daban-daban a cikin wata huɗu a jihar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Aliyu, ya fitar a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, 2023. ya ce a daidai wannan lokacin, an kama kimanin mutum 104 da ake zargi da aikata fashi da makami.
Kakakin rundunar ASP Aliyu, ya ƙara da cewa an kama mutum 97 da ake zargi da laifin ki-san kai, kuma an kama mutum 148 da ake zargi da aikata laifin fyade, sannan kuma an kama mutane bakwai da laifin mallakar haramtattun ƙwayoyi.
Har ila yau, a cikin wannan lokacin an ƙwato kayayyaki da suka haɗa da ƙaramar bindiga guda ɗaya, da harsasai 523.
ASP Aliyu, ya cigaba da bayanin cewa, sauran kayayyakin da aka ƙwato sun haɗa da bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu, bindigu na gida guda shida.
Wata majiya ta bayyana cewa rundunar yansandan sunsami nasarar ƙwato dabbobi sama da 600 da aka sace, motoci da babura 12 da ake zargin na sata ne da wayoyin hannu guda 17 da ake zargin na sata ne.
A cewarsa, wasu haramtattun ƙwayoyi da aka kwace a lokacin da ake binciken sun haɗa da buhu 568 na D5, ƙulli 180 na tabar wiwi, fakiti 23 na ƙwayar Exzole, fakiti 411 na ƙwayar Rebozel, da fakiti biyar na ƙwayar Diezole.