Majalisar Dattawan Najeriya ta lashi takobin gudanar da bincike kan harin kuskuren da rundunar sojin kasar ta kai, da ya janyo mutuwar mutane da dama a jihar Kaduna.
Kawo yanzu ba a fadi adadin wadanda suka rasa rayukansu ba, yayin da kuma wasu ke kwance a gadon asibiti ana kula da lafiyarsu.
Sanata Lawal Adamu Usman, (Mr La), shine dan majalisar dattawan Najeriya mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, inda aka kai harin, ya shaida wa BBC cewa al’amari ne da ba za su bari ya wuce ba:
“Wannan abu ne da ba za mu bari ya wuce ba, za mu sa a bincika a gano dalilin da ya sa ake samun irin wannan iftila’i . Mutane na yin ibadarsu a zo a jefa mu su bam, sai mun binciko abinda ya faru kuma a dauki mataki akan wadanda suka kai harin” in ji shi .
Gomman mutane ake fargabar sun rasa rayukansu bayan harin bam da jirgin saman yakin ya kai wa gungun masu Mauludi bisa kuskure a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi .
Sai dai duk da cewa yanki ne da ke fama tashin hankali sakamakon hare haren ‘yan bindiga amma majalisar dattawan Najeriya ta danganta alamarin kan gazawar sojojin kasar wajani wajan tattara bayanan sirri kamar yadda sanata Lawal Adamu Usman ya ce:
“Akwai gazawa wajan tattara bayanan sirri saboda ba bu yadda za a yi ka saki harsashi idan baka tabbatar da wurin da za ka kai harin ba ballantana bam. Bam babban abu ne kafin a sake shi dole sai an tabbatar da cewa masu garkuwa da mutane ne a wurin. Kuma idan har akwai sakaci to zamu tabbatar cewa an kama mutane kuma za’a hukuntansu “, in ji shi.
Tun farko gwmnatin jihar kaduna ta kafa kwamitin bincike da aka dorawa alhakin gano abinda ya faru.
Ita ma majalisar dattawan kasar ta ce za ta kafa kwamitin binciken akan alamarin tare da kai dauki ga mutanen da alamarin ya rutsa da su