Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta ce nan ba da jimawa ba za ta fitar da makaman da jami'anta suka ƙera.
Darakta Janar na hukumar, Yusuf Bichi ne ya bayyana haka ranar Asabar, a wajen bikin yaye tawagar jami'an da suka samu horo na musamman kan tattara bayanan sirri a Abuja babban birnin ƙasar.
Bichi ya ce nan ba da jimawa ba, DSS za ta fara ''ƙera abin da za ta yi amfani da shi, sannan ta yi amfani da abin da ta ƙera''.
Ya ƙara da cewa ''daga cikin makaman da hukumar ke shirin fitarwa, har da jirage marasa matuƙa''.
Daraktan hukumar ya kuma ce DSS za ta ci gaba da tallafa wa cibiyar nazarin harkokin tsaro ta ƙasar domin samun nasarar yaɗa iliman da za su taimaka wajen tabbatar da tsaro a ƙasar.
Ya kuma yi kira ga jami'an da suka yaye da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen kare ƙasar daga ayyukan ɓata-gari.