Gidauniyar tsohon shugaban majalisar dattijai ta ƙasa, Alhaji Abubakar Bukola Saraki, ta buƙaci al'umma da su haɗa kai wajen ganin an cicciɓa harkokin wasanni a ƙasar nan.
Gidauniyar wadda Saraki yake daukar nauyi ta bayyana haka ne a wajen buga wasan ƙarshe na gasar ƙwallon kwando ta Hilltop Pacers Basketball da akayi a ranar Alhamis.
"A gidauniyar Abubakar Bukola Saraki muna son wasan ƙwallon kwando kamar yadda shugaban gidauniyar shi ma yake sha'awa" kamar yadda sanarwar ta bayyana
"Dakta Abubakar Bukola Saraki mutum ne wanda yayi amanna cewa wasanni suna taka muhimmiyar rawa wajen samar da ingantacciyar rayuwa. A kullum maganar sa ita ce yadda za a zaƙulo matasa masu sha'awar wasan domin su samu ci gaba".
Sanarwar ta ƙara da cewa "Hakanne ma yasa jiya, wannan gidauniya ta samu halartar zuwa wajen wasan ƙarshe na wasan ƙwallon kwando ta Hilltop Pacers Basketball. Kallon waɗannan matasan suna jajircewa yana da ban sha'awa sannan yadda ake zura ƙwallon a cikin kwando shima abin burgewa ne da ƙarfafa gwiwa.
Gidauniyar na son ganin ta cike giɓin da yake tsakanin waɗannan matasan ƙwallon kwandon, sannan an samar musu da dama da yanayi mai kyau wanda zai sa su nuna bajinta da ƙwarewarsu, har ila yau su cimma burikan su.