Inda suke ƙalubalantar hurumin Kotun daukaka kara na neman yin sauyi a rubutaccen hukuncin da ya tabbatar wa Abba kujerarsa ta Gwamnan Kano.
A halin da ake ciki wasu lauyoyin sa-kai sama da 200 sun fito za su kare Abba da NNPP a Kotun Koli domin ganin kujerarsa ta tabbata.
A daya ɓangaren kuma lauyoyi kimanin 500 ne suka ce za su kare APC da Gawuna domin ganin Abba ya bar gidan gwamnati.
A ranar 20 ga Nuwamba, kotun kotu sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan Kano ta kwace kujerar Gwamna Abba bayan ta soke dubu 165 da doriya daga kuri’un da ya samu, a matsayin haramtattu, saboda rashin sa-hannu da hatimin INEC a kansu.
Hakan ya sa Gwamna Abba da NNPP suka garzaya zuwa Kotun Daukaka Kara ta Tarayya Najeriya domin neman adalci.
Daga nan kuma suka kara daukaka kara zuwa Kotun Ƙoli, wadda suka shaida wa cewa kuri’un da APC ta tantance marasa sa-hannu da sitamfi ba su ma kai 20,000.
Don haka suna kalubalantar soke kuri’un Abba dubu 165, wanda ta ba wa Gawuna damar shan gabansa a wajen aan kuri’u.
Yanzu dai abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a kotun koli.