Jamilu Lawan Yakasai guda ne daga cikin hazikan ma'aikatan kamfanin jarida ta Raihana, yasa rabauta da mikamin P.A mataimaki na musamman ga mataimakiyar shugabar gidan talabijin na Abubakar Rimi wato "ARTV.
Lallai ansanya kwarya a gurbinta, kafin nan Jamilu Yakasai ma'aikaci ne a gidan rediyo na nasara, a madadin kafatannin ma'aikatan wannan gida muna tayashi murnar wannan samun cigaba daya kara yi, Allah yasanya albarka.