Alfijir labarai ta rawaito rahotanni sun bayyana cewa, Akeredolu wanda ya shafe kusan shekaru takwas yana gwamnan jihar Kudu maso Yamma ya rasu a wani asibitin Legas. sakamakon kamuwa da cutar sankarar bargo.
A ranar 13 ga watan Disamba, gwamnan ya sake komawa hutun jinya. Bayanin hakan ya fito ne a wata sanarwa dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran sa, Richard Olatunde, inda ya jaddada kudirin gwamnan na ba da fifiko ga lafiyar sa da kuma samun cikakkiyar lafiya kafin ya ci gaba da aikinsa.
Yayin da Akeredolu ba ya nan, mataimakin gwamnan, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya dauki nauyin gwamnan a matsayin mukaddashinsa, kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana.
Kafin tafiyar tasa na baya-bayan nan, gwamnan ya koma bakin aiki a watan Satumba, bayan karin hutun jinya da ya yi a kasar waje wanda ya fara a watan Yuni.
Sai dai rashin sanin halin lafiyarsa ya haifar da dambarwar siyasa yayin da yake ci gaba da gudanar da al’amuran jihar Ondo daga gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Tsare-tsare na nesa ya haifar da dagula dangantaka tsakanin magoya bayan Akeredolu da mataimakin gwamna Aiyedatiwa, wanda ya kai ga yunkurin tsige mataimakin gwamnan kafin da kuma bayan tafiyar Akeredolu.