Gwamnan yayi nadin a Daren jiya laraba, kamar yadda kakakin Gwamnatin Kano Hon Sunusi Bature Dawakin Tofa ya wallafa a shafinsa na fasbok,
Hajiya Hauwa Isah Ibrahim ta kasance tsohuwar ma'aikaciya a gidan talabijin na Abubakar Rimi, bayannan ma'aikaciya ce a gidan rediyo nasara dake Kano, wacce take bangaren sashin shirye-shirye,
Bayannan itace shugaba ta bangaren DCA ta kasance tana gudanar da kasuwanci daban-daban.
Hajiya Hauwa tasance mutuniyar kirki wanda kowa ke sanyin mu'amula da ita, suma ma'aikatan gidan talabijin na Abubakar Rimi ARTV sunbayyana farincikin su game da wannan mukami da Gwmanatin Kano tayi mata.
Gwamnan yabada umarnin fara aiki nantake.