Da yake jawabi yayin sanya hannu kan kasafin kudin wanda ya haura sama da Naira biliyan 437, gwamna Abba Kabir Yusuf yace kasafin kudin zai fara aiki ne a watan Janairun shekara Mai kamawa.
Yace an ware kaso sittin da hudu cikin dari domin aiwatar da manyan ayyuka, yayin da ayyukan yau da kullum aka ware musu kaso talatin da shida cikin dari na kasafin.
Gwamna Abba Kabir Yusuf yace kasafin kudin zai kawo ci gaba ta fuskar Ilimi da lafiya da noma da ayyukan raya kasa tare da bunkasa tattalin arzikin alumar jihar Kano.
A nasa bangaren shugaban majalisar dokoki ta jiha Alh. Jibril Ismaila Falgore ya ce al'umur jihar Kano zasu ga sauye-sauye masu ma'ana a fadin jihar nan.