Gwamnatin jihar Kano ta sanar da sauya sunan Ƙaramar Hukumar Kunchi zuwa Ƙaramar Hukumar Ghari.
Wannan sanarwar na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da majalisar dokokin jihar Kano ta aika wa babban sakataren ma'aikatar da ke kula da ƙananan hukumomi da masarautu ta jihar ranar 14 ga watan Disamba, 2023.