Yayin da take ci gaba da shan suka game da yawan wakilan ƙasar a taron COP28, gwamnatin Najeriya ta ce mutum 422 kacal ta ɗauki nauyi daga cikin wakilai 1,411 da suka halarci taron a Dubai.
Tun a ƙarshen mako ne 'yan Najeriya suka dinga sukar gwamnatin APC ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu bayan ta bayyana cewa wakilan da suka je daga Najeriya sun zarta 1,000 a taron na shekara-shekara kan sauyin yanayi.
Sai dai cikin wata sanarwa da Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya fitar a yammacin yau Litinin ta ce 422 kawai aka zaɓo daga fadar shugaban ƙasa, da Majalisar Sauyin Yanayi ta Ƙasa, da ma'aikatar muhalli, da sauran ma'aikatu, da ofishin mataimakin shugaban ƙasa, da majalisar tarayya.
"Wakilcin Najeriya ya dace da matsayinmu na shugaba wajen yaƙi da sauyin yanayi a Afirka," in ji ministan.
Ya ce sauran mutanen da suka halarci taron daga Najeriya sun fito ne daga ɓangaren 'yan kasuwa, da ƙungiyoyin farar hula, da 'yan sa-kai, da gwamnatin jihohi, da 'yan jarida, da cibiyoyin ilimi, da sauransu.
Ga jerin ma'aikatun da gwamnatin tarayya ta tattaro wakilan da kuma adadinsu:
1. Majalisar Sauyin Yanayi ta Ƙasa (National Council on Climate Change) = 32
2. Ma'aikatar Muhalli = 34
3. Dukkan ma'aikatu = 167
4. Fadar shugaban ƙasa = 67
5. Ofishin mataimakin shugaban ƙasa = 9
6. Majalisar tarayya = 40
7. Ma'aikatu da hukumomin tarayya = 73