Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Alh. Abba Kabir Yusuf, ta ƙaddamar da Manhaja mai suna "Shawarata" wacce al'ummar jihar zasu iya shigar da Rahoton kai tsaye akan wata rashawa ko kuma bada shawarar.
Hukumar karɓar korafe-korafen al'umma da yaƙi da rashawa ta jihar Kano "Anti Corruption", karkashin jagorancin shugabanta Barista Muhuyi Magaji Rimin Gado ne ya ƙaddamar da Manhajar a safiyar ranar Asabar,
A yayin taron bikin ranar yaƙi da rashawa ta Duniya da aka gudanar a dakin taro na Coronation dake fadar Gidan gwamnatin Kano.
Gwamnan Kano wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, yace an kirkiri Manhajar ne domin tabbatar da yin Gwamnati a bude, ta yadda al'umma zasu kawo rahoton wata rashawa da su ka gani domin a dauki mataki.
Taron yasami halattar manya-manya baki dama al'ummar Jihar