Hukumar Hisbah da takwararta da ke kula da, Gidan adana Dabbobin Daji, watau gidan Zoo na jihar kano sun kamala shiri tsaf dan inganta alakar aiki a tsakanin su dan kawar da yada dabi'u da ka iya gurbata tarbiya da al'ada,
Musaman a lokacin bikin sallar kirsimeti da ta sabuwar shekarar miladiya da ke gabatowa da ma sauran bukukuwa a nan gaba.
Wakiliyar mu Fiddausi Bello Ishaq ta rawairo cewar Mai rike da Mukamin babban kwamandan hukumar Hisbah kuma babban Daraktanta (DG), Alhaji Abba Sa'id Sufi shine ya sanar da hakan ta cikin jawabinsa a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar jami'in da ke kula da gidan Zoo,
Karkashin jagorancin Shugaban hukumar, Alhaji Sadik Muhammad kura a shalkwatan hukumar da ke unguwar Sharada kano.
Alhaji Abba Sa'id Sufi ya ce inganta alakar aikin zai bawa hukumar Hisbah daman sanin irin bukukuwa da tarurraka da jama'a ke gudanarwa baya ga sa ido a tsakanin ma su kai ziyara gidan Zoo dan saman shakatawa.
Ya kuma yi alkawarin sa ke tura karin jami'ia a karamin ofishin Hisbah da cikin gidan Zoo, ma su cike da kwarewar aiki, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.
A na ta jawabin martaba kalai, mataimakiyar, babban kwamandaniyar, mata watau (DCG Women) Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta bai ya na farin ciki da ziyaran.
Dr. Khadija Sagir Sulaiman ta bukaci Shugaban hukumar da ke kula da Gidan adana Dabbobin Daji watau gidan Zoo da ya dauki mata aiki a hukuman duba da mata da yara su ne su kafi kai ziyara a kowane lokaci gidan Zoo.
Tun da fari a jawabinsa Shugaban hukumar kula da Gidan adana Dabbobin Daji watau gidan Zoo, Alhaji Sadik Muhammad kura ya ce makasudinsa na zuwa hukumar Hisbah shine inganta alakar aikin a tsakanin hukumomin guda biyu tare da zamantar da yin aiki tare.
A lokacin ziyaran ya roki hukumar Hisbah da ta kara yawan Dakarunta da ke aiki a gidan Zoo, duba da yadda su ke gudar da aiki cikin kwarewa, tare da al'barkawarin ba da hadin Kai da goyon baya.