A cewar mai taimakawa Kwamishinan Shari'a na Jihar Kano Amir Abdullahi Kima Darmanawa wannan maganar karar da wasu yan kasuwa suka kai Gwamnatin Jihar Kano Babbar kotun Tarayya dake Abuja (Federal High Court) inda ta bada umarnin rufe asusun Gwamnatin Jihar Kano har sai ta biya Naira Biliyan 30 diyya ga Yan Kasuwar,
To ya kamata mutane su fahimci Babu wata kotu da take da hurumin sauraron wannan kara, sakamakon tin hukuncin farko da kotun tayi, Gwamnatin Jihar kano ta daukaka kara domin neman kotun daukaka kara ta dakatar da hukuncin kotun.
Kuma har yanzu kotun daukaka kara bata bada hukunci ba, sabo da haka wannan muna zargin yan Gandujiyya ne suka bi ta gurbatacciyar hanya domin su raba hankalin Gwamnati.
Amma ina mai tabbata da da Jama’ar Jihar Kano wannan ba wani abubane wannan kotu bata da hurumi har sai kotun daukaka kara tayi hukunci Sannan zasu samu damar tafiya kotun gaba.
Muna rokon Allah Ya cigaba da taimakon Jihar Kano ka nisan tata da gurbatattun mutane.
Amir Abdullahi Kima Senior Special Reporter Justice to the executive Governor of Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf
06/12/2023