A martanin da ya mayar dangane da ce-ce-ku-cen Da ake tayi dangane da hukuncin da kotun daukaka kara da ta yanke na hambarar da gwamna Abba Yusuf na jihar Kano, babban lauyan lauya Mike Ahamba, SAN, ya nuna damuwa.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito, kwamitin mutane uku na kotun daukaka kara ya amince da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano ta yanke inda ta bayyana Dr. Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai kuma binciken da aka yi na hukuncin ya nuna an samu sabanin ra’ayi, inda a karshe Hukunchin ya nuna goyon bayansa ga gwamna Yusuf yayin da dalilan yanke hukuncin suka tafi kansa. Duk da wannan, kotun daukaka kara ta yi watsi da sabanin a matsayin kuskuren alkalalai, inda ta tsaya kan matakin da ta dauka na tsige gwamnan.
Mike Ahamba, SAN, ya jaddada muhimmiyar rawar da bangaren shari’a ke takawa, inda ya ce, “yakamata mu sanar dasu cewar muddin bangaren shari'a ya lalace to mun shuga uku Kuma an gama duk wani abu da ake Kira shari’a, su sani cewa kuma idan an gama shari’a,l to duk mun gama. Yakamata duk su san haka.
“Na san cewa abubuwa sunjima da Fara lalacewa tun a baya. Ba yau aka fara ba. Anyi mana haka Ni da Buhari a 2003 da 2007. Amma ba ka ruguza gidan da ka san kana ciki.
“Idan aka ruguza bangaren shari’a, amsar daya ce kawai rashin zaman lafiya Kuma rashin zaman Lafiyar mai haɗarin gaske tunda mafi ƙarfi shike kwatar mulki. Idan akwai abubuwan da ke faruwa, don haka tun wuri ya Kamata mu gyara abubuwanmu akan ta hanyar bin doka da oda.
“Bai Kamata munaji Muna gani bu bar kowa ya lalata cibiyar harkokin shari'a ba saboda muna bukatarta fiye fa komai.Dole ne masu ruwa da tsaki su yi kokarin gyara lamarin.”
Ahamba ya yi kira da a hada karfi da karfe wajen ganin an magance matsalolin da aka kafa a tsarin shari’a maimakon yin kasadar tabarbarewar bangaren shari’a.