Ana ci gaba da nuna tsananin alhini, a lokacin da ake kokarin tantance yawan mutanen da suka mutu a wani mummunan luguden wuta da ya kai kan wasu masu taron Mauludi a Tudun Biri cikin yankin karamar hukumar Igabi.
Wani shaida ya bayyana wa BBC cewa cikin tsakar dare ne wani jirgin sama ya jefa musu bam suna tsakiyar bikin Mauludi.
"Mun kuma je, muna son mu tsame wa'inda ba su cika ba, da ke neman taimako, to an fara jawo wa'inda suke da sauran rayuwa, kuma jirgin again ya kuma dawowa ya jefa bam din."
Bello Shehu Ugara ya ce cikin wadanda suka mutu akwai mata da kananan yara har ma da jarirai.
A cewarsa, jirgin ya yi ta shawagi a kan mahalarta Mauludin kafin ya jefa musu bam a karon farko da misalin karfe 10 na dare.
Shaidan ya bayyana fargabar cewa mutanen da suka mutu sun kai gommai a iftila'in.
Rundunar sojin saman Najeriya tuni ta fitar da sanarwa, tana musanta duk wani hannu a wannan al'amari.
Sai dai, gwamnatin jihar Kaduna ta tabbatar da faruwar luguden bam din a kan "mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba". Ta kuma bayyana shi da cewa abin takaici ne matuka.
Bello Ugara ya ce jirgin ye jefa bam din ne a daidai wata bishiyar mangwaro, inda suke halartar taron.