Mai magana da yawun rundunar, Edward Gabkwet ne, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Ya ce dukkan wadanda ke cikin jirgin sun kubuta, ko da yake sun samu “kananan raunuka”.
Jirgin helikwaftan kirar MI-35P ya yi hatsari ne da misalin karfe 7.45 na safe, jim kadan bayan ya tashi a kan hanyarsa ta zuwa yaki da masu zangon ƙasa ga tattalin arzikin kasa da ke fasasa bututu suna satar man fetur a jihar Ribas.
“Abin farin cikin shi ne dukkan ma’aikatan jirgin 5 sun kubuta da rayukansu, sai dai kananan raunuka kuma a halin yanzu ana kula da su a wani asibitin sojoji da ke Fatakwal.
“Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar, a halin yanzu yana kan hanyarsa ta zuwa Fatakwal, don ganin halin da ake ciki da kansa, kuma da niyyar duba lafiyar ma’aikata,” in ji sanarwar.
Gidan talbijin na Channels ya ce yawaitar hatsari da jiragen saman sojin Najeriya ke yi wanda ke janyo asarar rayuka, ya zama abin damuwa matuƙa a cikin shekara biyu, inda masu ruwa da tsaki suka yi kira ga sojoji, su kiyaye hanyoyin gudanar da ayyukansu da kuma kula da jiragensu na yau da kullum.
A watan Agustan 2023 ma, jirgin saman sojin Najeriya NAF MI-171 ya yi hatsari a kusa da kauyen Chukuba na jihar Neja, inda ya haddasa asarar sojoji.
A 2021, sojoji akalla 20 ne suka rasu cikin wata uku a hadurra uku na jiragen saman sojin Najeriya.