Kalmar da wasu matasa ke addabar 'yan mata da sunan barkwanci ko kuma shakiyanci takai ga nada akan wani matashi.
Wata mata tana cikin tafiya a gefen titi, sai wannan matashi ya bita yana ta ce mata, "Kin Iya Kunu", har ya fusata ta, taje ta shigar da korafi a Ofishin 'Ƴan Sanda.
Kamar yadda jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yansandan kano Sp Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa, yanzu haka wannan matashin yana tsare a bayan "Kanta".
Wasu nagannin wannan kalmar batsace da akwai rashin tarbiyya wajen fadarta, wasu kuwa nagannin kawai barkwanice, to koma dai mecece jama'a sai a kiyaye domin takai wani ga " danasani".
Gani ga wane ...