Yayin wani taron manema labarai a ranar Juma'a, inda yake mayar da martani kan tambayar da wani ɗan jarida ya yi masa, Shugaba Evariste Ndayishimiye ya ce Burundi ba ta buƙatar tallafin manyan ƙasashe masu ƙarfin iko "su riƙe taimakonsu" idan dai yin hakan na tare da sharaɗin a bai wa 'yan luwaɗi da maɗigo 'yanci.
A jawabin nasa, shugaban ya yi misali da Littafin Injila, inda ya ce Ubangiji ya yi hani da neman jinsi kuma ya ce neman jinsi kwata-kwata ba ma maganar da ake tattaunawa ba ce a ƙasarsa ta Burundi.
"A wajena, ina ganin idan muka ga masu irin wannan aƙida a Burundi, a kai su filin wasa a jefe su, kuma yin hakan ba zai zama laifi ba," cewar shugaban ƙasar Burundi.
Mista Ndayishimiye ya ce luwaɗi da maɗigo kamar yin zaɓi ne tsakanin hanyar shaiɗan da ta Ubangiji".
"Idan kana son zaɓar Shaiɗan, toh ka je ka yi rayuwa a irin ƙasashen, kuma ina tunanin masu fafutukar zuwa can suna son rungumar ɗabi'un, ya kamata su tsaya a can kada su kuskura su kawo mana su." in ji shugaban.
Burundi dai ta haramta neman jinsi kuma laifi ne da ke iya janyo hukuncin ɗauri na kusan shekara biyu a gidan yari.
A watan Agusta, mutum bakwai aka yankewa hukuncin shekara tsakanin daya zuwa biyu a gidan yari bayan kotu a Gitega ta same su da laifin neman jinsi, ko da yake,sun musanta tuhumar.