A cikin wata sanarwa da mataimakinsa na musamman a kan kafafen yada labarai, Abba Ibrahim Wada ya fitar, Saraki ya ce ya zama dole ayi bincike domin gano wadanda suka aikata wannan abu sannan a dauki matakin hana faruwar irin hakan a nan gaba.
"Kashe mutane ta hanyar harba musu bom da akayi a lokacin da suke bikin Maulud a kauyen Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna abin takaici ne".
"Da ni da iyali na muna mika sakon ta'aziyyar mu ga al'umma da gwamnatin jihar Kaduna da iyalan wadanda wannan ibtila'i ya fadawa. Ina addu'ar Allah ya jikan wadanda suka rasu sannan wadanda suka samu rauni kuma Allah ya ba su lafiya.
"Sai dai bayan wannan Mummunan ibtila'i, ya zama dole mu gujewa faruwar irin wannan a nan gaba. Sannan akwai bukatar a gudanar da bincike domin a gano yadda wannan abin ya faru sannan a kawo hanyoyin gujewa faruwar sa nan gaba.
Har ila yau, ya zama dole a sake nazari, wannan ya zama izina, bugu da kari a hada hannu waje guda wajen sake gina kishin kasa a zukatan mutane, adalci da kaunar juna domin tabbatar da kiyaye lafiyar duk wani dan kasa.
Abba Ibrahim Wada
Media Aid to the former Senate president,
Alhaji Abubakar Bukola Saraki