Kadan daga cikin binciken dana gudanar da Kuma Hirarraki ( programs) da mukai da masana tattalin arziki tun bayan bullar sanarwar da SHOPRITE ta yi na cewar nan da watan Junairun2024 zasu fice daga kano. Radio da daidaiku.... Masanan sun bayyana cewa rufe ShopRite zai taba tattalain arzikin jihar kona sosai domin hakan zai sanya shakku cikin zukatan masu son zuwa kano zuba jari a harkar kasuwanci duba da cewar kamfani kamar ShopRite wanda kasuwace mai zamanta ta rufe balle kuma wanda baisqn dawar garin ba.
FILM HOUSE CINEMA!.
Kasuwar film (feature) kusan zamani ya shudar da ita musamman a arewa wanda hakan tasa zuwan ShopRite masu shirya film suka rungumeta duk da kasancewar wasu na ganin cewar anan abun nan ne da bahaushe kecewa " Kura da sham bugu, kato ta karbe kudi" amma dai ta taimaka wajen sanya wasu fina-finan hausa fice a duniyar film kuma ta daga jarumai da dama kazalika, masu shirya fina-finan hausa sun daukaka sun samu lambar yabo da girmamawa ..
Kadan daha cikin fina-finan da zan iya tunawa akwai
MARIYA, MANSOOR, HALIMATUSSADIYA, MATI A ZAZZAU, TAURARON BOYE, ABARWA RAI, KALAN DANGI, AISHA, FATI, KAMANNI, SARKI GOMA, KOKAI NISAN DARE...
Mashirya fina-finan daga ciki akwai.
@realabmaishadda @realalinuhu @official_tyshaban @yaya_muhammad1 @rahamasadau da sauransu...
Kusan ADO BAYERO MALL ce kadai cinema ta zamani kafin zuwan Platinum Cinema wacce fina-finai biyu zuwa uku kawai aka haska!
Cinema nada matukar muhimmanci ga ko wacce masana'antar film kuma tana daukaka darjar masana'antar... Wanda rufe ShopRite zai taba cigaban masana'antar a idom duniyar film..
WACCE KASUWA TA RAGE!
Na san zakuce YOUTUBE! To naji... Amma nawa kuke kashewa a YouTube nawa kuke samu? Shin kuna mayar da kudinku? Mutum nawane suke iya mayar da kudinsu? Ko gidan Tv zakuje ku sai airtime domin tabbas ana saya kuma mun sani? Mecece mafita?
Ni a karan kaina! Mafita... Ya zama wajibi al'umar arewa suyi investing a harkar cinema domin ko anso ko anki, bayan Noma babu abunda yakai Kannywood bawa matasa aikinyi a Arewacin najeriya kuma rufewar kasuwar film irin ado bayero Mall koma bayane ga masana'antar!