Tunda fari dai wani mutum mai suna Auwalu Usman ya shigar da karar cewar wasu mutum hudu suna shiga masallaci suna harkar luwadi da shaye-shaye a cikin masallaci. Yace lokacin dayayi yunkurin hanasu sai suka taru sukai masa dukan tsiya, tare da yi masa barazanar cewar yayi musu shisshigi cikin rayuwarsu.
Mai gabatar da kara Aliyul Abideen ya karanto musu kunshin tuhumar, wanda ake zargi na farko ya amsa ya amsa lafinsa, sai kuma ragowar Ukun suka musanta.
Daga karshe kotun ta bada umarnin acigaba da a jiye su a gidan a jiya da gyaran hali har zuwa ranar 3 ga watan Junairun shekara mai kamawa, domin cigaba da sauraren karar.