A daidai lokacin da Mike shirin bankwana da shekarar da muke ciki ta 2023, Majalisar dokokin Jihar Kano ta amince da kasafin kudi na shekarar dubu biyu da ashirin da hudu da Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ya gabatar a gabanta.
A wannan rana ta laraba ce majalissar ta sahalewa gwamnan Kano Alh Abba Kabir Yusuf da kasafin kudin,
Kasafin da ya shafin muhimman ayyuka na bangaren ilimi, noma, titina lafiya da dai makamantansu.
Inda a wannan rana ake sa ran gwamnan zai kaddamar da harsashin gadar kasa ta dan'agundi da kuma gadar tal'udu.