Majalisar wakilai ta ƙasa za ta gudanar da bincike kan harin Boma-Bomai da rundunar sojin Najeriya ta kai was masu bikin Maulidi a Garin Tudun Biri dake ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna bisa kuskure.
Shugaban kwamitin tsaro na majalisar, Babajimi Benson ne ya tabbatar da haka ranar Asabar a babban Birnin tarayya Abuja, inda yace lamarin ya matuƙar tayar musu da hankali, saboda haka dole suyi bincike.
Dan majalisar ya kuma yi kira ga jami'an tsaro da su tabbatar da walwala da kare kare rayukan al'ummar ƙasar.
Tun lokacin da abun yafaru da shugabanni da malamai da dama na sassan kasar nan ne suke shiga wannan gari domin gabatar musu da ta'aziyyar wadanda suka rasu, dama jaje ga wadanda suka sami jikkata