Matashin ya nemi kudi Naira Miliyan Daya 1 a matsayin kudin fansa, sai dai abun bantakaici da shi mai garkuwar ake yawo neman yaron daya 6ata,
Kuma da shi ake kar6ar gaisuwar jajen 6atan yaron, bayan da bincike yayi nisane aka sami yaron da akai garkuwa dashi a Unguwar Gwammaja dake yankin karamar Hukumar Dala cikin birnin Kano.
Bayan da salisu yashiga hannun jami'an rundunar 'yansandan Kano ne yace yayi hakane sakamakon iftila'in rugujewar kasuwancinsa da yayi na kudi sama da Naira Dubu Dari Biyu 200,000.
Yanzu haka Jami'an yansanda Kano dake Helikwatar bamfai sun mika yaron zuwa ga Mahaifinsa, inda mahaifin yaron ke cike da farinciki dama bayyana godiyar sa da Jami'an 'yansandan bisa jajircewarsu na samun yaronsa.
Daga karshe dai Rundunar 'yansandan Kano sunce da zarar sun kammala bincike zasu mika wanda ake zargi zuwa kotu domin tabbatar da anyi masa hukuncin daya dace.