Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar cafke wani kasurgumin dan Daba , Ibrahim Rabi’u wanda akafi sani da Janare, da yaransa guda 7 da ake zargi da addabar al’umma.
A ranar 9 ga watan Nuwamban 2023, Janare ya jagoranci wasu gungun yan daba sama da 200, wadanda suka tare hanyar Kano zuwa Katsina , inda suka yi wa matafiya kwace da fashi tare barnata dukiyar al’umma.
Wasu da suka fada hannun Janare, sun bayyana wa yan sanda cewa,yan dabar sun dinga karbar Naira duba daya 1,000 daga wajen su kafin su wuce.
Al’ummar Kurna, Bachirawa, kwanar Ungoggo da kuma matafiya sun shiga damuwa kan aika-aikar da gungun yan dabar ke aikata wa a lokuta daban-daban.
Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce tun bayan samu labarin faruwar lamarin, kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel, ya tashi dakarun yan sanda dake yaki da aikata laifukan Daba, karkashin jagorancin SP Hussaini Gimba , wadanda suka bazama tare da samun nasarar cafke Janare da yaransa a wani sumame da suka kai.
Sauran sun hada da Aminu Adamu Bachirawa, Halifa Bashir Kwanar Ungoggo, Jamilu Mas’ud Kwanar Ungoggo, Abubakar Surajo Bachirawa, Ahmad Surajo Bachirawa, Muftahu Surajo Bachirawa da kuma Ibrahim Surajo Bachirawa.
SP Kiyawa ya ce cikin kayan da aka samu nasarar kwato wa daga wajen su , sun hada da Babura marasa namba guda 2, Barandami guda 3, Adduna 4, Sinkin tabar Wiwi 5, Exol Tablets guda 135, Sholusho guda 150, Diazepam 10 da kuma Allurar Potwin guda 27.
A karshe rundunar ta tabbatar da cewa , da zarar ta kammala gudanar da bincike za ta gurfanar da su a gaban kotu.