Rundunar 'yan sandan Kano ta fitar da sunayen wasu 'yan daba 72 da take nema ruwa a jallo bisa zargin aikata laifin fashi da makami da daba.
Mutanen suna cikin tubabbun 'yan daba 623 da suka mika wuya ga 'yan sanda a kwanakin baya, karkashin shirin zaman lafiya da yi musu afuwa.
Rundunar ta ce ta gano wani da ya mika kansa a baya, a yanzu yana jagorantar gungun wasu matasa suna tayar da hankalin mutane a unguwanni harma da yankin Dala.
Ga jerin sunayen 'yan daban:
1. Bahago Afah Kuka Bulukiya
2. Malam Keya Dogon Nama
3. Habu Mayo Kuka Bulukiya
4. Dan Mama Adakawa
5. Alhajin Bilal Lungun B/malam Madabo
6. Buda Karofin Dala
7. Alhaji Baba Shirawa
8. Abba Gashi Gashi Dandinshe Tasha
9. Hassan Cisse Rijiya Biyu
10. Dan Kamsusi Dandinshe
11. Likuman Makafin Dala
12. Saddiku Style Gadar Salga
13. Kwaja Dandinshe
14. Malam Rodi Dala Makarantar Nafahatu
15. Halifa Dan Asabe Shatsari
16. Bagiya Shatsari
17. Abba Ali Mugu Sanka
18. Dan Kyahun Rijiya Biyu
19. Nabara’u Madigawa
20. Habu Udukul Madigawa
21. Fato Madigawa
22. Haruna Musa Jibrin Madigawa
23. Malam Shehu Madigawa
24. Dahuwa Chediya
25. Fiya Dandinshe
26. Dubulliya Aikawa
27. Sharu Sharna Rijiya Biyu
28. Bukari Tijjani Dala
29. Dan Auwalu Kwanar Dala
30. Dan Chaina Kul-kul
31. Shangwa Rimin Abba Kul-kul
32. Dan Yellow Chediya
33. Abba Kan Fulogi Rijiya Biyu
34. Dilin Dala Layin Sarka Gurgu
35. Dandolo Lungun Kotu
36. Master Lungun Kotu
37. Dogo Kantin Uba Angwaye Titin Alfanda
38. Bala Kwalli Kantudu
39. Ala Baka Bakin Kasuwa Maskwani
40. Ummo Lungun Kotu
41. Walidi Lungun Yankifi
42. Guguwa Yalwa
43. Bisi Yalwa
44. Yartakabiruwa Yalwa
45. Ubaidu Kantudun Madabo
46. Shatoli Filin
47. Dan Isa Shirawa
48. Kabiru KB Show Bayan Dala Lungun Nafahatu
49. Nurere Lungun Kotu
50. Abba Ho Filin Faroma
51. Saddiku Savio Filin Kutare
52. Wando Filin Kutare
53. Yahaya Army Lungun Nafahatu
54. Mubarak Bade Lungun Nafahatu
55. Dan Umar Ziri Zirin Gyaranya
56. Abdul Lokon Makera Shatari
57. Addahir ( Dahri) Dirimin Daje
58. Tere Dirimin Daje
59. Annani Karofin Daganda
60. Tata Kantudu
61. Dan Sani Falo
62. Oris Kantudu
63. Tsulum Lungun Kankarofi
64. Mamman Kantudu
65. Malo Kantudu
66. Al-amin Makafin Dala
67. Tulu Dala
68. Abba Idan Dala
69. Tahani Lungun Yan Kifi
70. Kilo Dala
71. Dan Jamilu Adakawa
72. Dan Turkwi Adakawa
CP Muhammad Gumel, ya ce wadannan mutane da ake zargi suna fito wa ne suna tsoratar da al’umma dan su aikata mu su fashi.
Ya kara da cewa, makonni biyu kenan da fara samun labarin gungun matasan, da suka fito da wani sabon salo dan razanar da jama’a ta hanyar wasa wukake a kan tituna su firgita jama’a su gudu gidajen su, sannan su kuma su aikata mugun nufinsu na sace-sace da dai sauran laifuka.
Kwamishinan ya ce wannan lokacin ba na yin afuwa ba ne, lokaci ne na yin fito-na fito da su a duk inda aka gansu.