Kakakin Rundunar 'Yansandan Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, yace wadanda ake zargin sun sato wayoyin salular ne daga garin Yanya Mararraba a Jihar Nasarawa don su kawo Jihar Kano su sayar,
Ranar 17 ga watan Disambar shekarar 2023 ne, dakarun yansandan suka samu bayanin sirri kan batagarin matasan su biyu, da suka hadar da mai suna Abba Aminu mai shekaru 23, mazaunin Lungun Sharifai dake Unguwar Kofar Mata ta Kano, da kuma Zulkifulu Bello mai Shekaru 30 Mazaunin Pantami tashar Mota ta Jihar Gombe.
An samu wayoyin kira daban-daban har guda 39, Rundunar 'yansandan tace da zarar ta kammala bincike zata mika wadanda ake zargi gaban kotu domin girbar hukunci.