Mai Martaba Sarkin ya ayyana korar ne ga manema labarai a fadarsa, a lokacin da ya ke wasu nade-naden sarautu a karshen mako.
Jaridar yanar gizo ta Mobile Media Crew ta rawaito Sarkin na cewa, korar shirin ya biyo bayan keta wasu ka’idoji addinin Musulunci da shirin ke kokarin yi a jihar da kuma zargin kokarin bata tarbiyar 'ya'ya mata da ke karatu a makarantu
Ya ci gaba da cewa shirin na kokarin wuce gona da iri wanda a matsayinsu na iyayen kasa, ba za su lamuncewa hakan a cikin kasa ba.