Ganduje ya hadu da Kawu Sumaila a yau.
Shugaban jam'iyar APC na kasa Dr Abdullahi Umar Ganduje ya halarci bikin rantsar da tsohon Gwamnan Jihar Plateau Sanata Simon Bako Lalong,
Wanda a yau aka rantsar da shi a matsayin Sanata bayan yin nasara da yayi a kotun zabe. Lalong ya ajiye kujerar sa ta ministan kwadago domin zama sanata.
A yayin bikin Rantsuwar Kawu Sumaila yaje inda Gandujen ke zaune suka gaisa duk da banbancin Jam'iyya dake tsakanin su.