Fitaccen wakaki kuma jarumi a masana'antar kannywood Garzali Miko yace tabbas almajiranta ne makasudin shigowarsa Jihar Kano,
Garzali Miko wanda tauraruwarsa ke haskawa a halin yanzu, yace shi dan asalin grain ringim ne ta Jihar Jigawa, bayan rasuwar mahaifiyarsa mahaifinsa ya kawoshi Kano, da 'yan uwansa domin suyi karatun tsangaya.
Sai dai Miko yace kafin yafara wasan Hausa yana kafa da kafa harzuwa wajen da yan fim ke taruwa domin ya kallesu a fili kawai, inda yace bayan ya nuna sha'awarsa da shiga harkar fim ne kuma kawunsa wanda shine marikinsa a Kano yace shi bai gamsu daya shiga fim ba.
Inda kawunnasa yace yafisan Garzali Miko yayi karatun zamani, nanne fah shi Garzali ya gudu zuwa Lagos harma yafara sana'ar sayar da gwalagwajin kayan miya, bayan yadawo Kano ya kara nuna muradinsa nasan shiga fim dindai kawunnan nasa yace shifa bai amince ba.
Nan fa Garzali ya kara guduwa Lagos komawarsa ke da wuya yafara yiwa wani makaho jagora inda suke shiga lunguna da sakon Jihar suna barace-barace, bayan dawowarsa Kano kuma yafara yasarwa da wasan Hausa ruwan Fiyawuta da jinja.