Yadda Dan Majalisar Tarayya na Jam'iyyar NNPP mai wakiltar Kiru da Bebeji na Jihar Kano kuma kakakin Sanata Kwankwaso Hon Abdulmuminu Jibril Kofa ya wallafa a shafinsa na Twitter.
Cewar Yau da safe, ni da takwarana Sanata Abubakar Sani Bello da Ministan Harkokin Waje, Amb. Yusuf Maitama Tuggar, mun gana da Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a Fadarsa da ke Abuja, inda muka tattauna manufofin Shugaban kan harkokin waje.
Sai dai bayan wannan tattaunawa Hon Kofa ya kara da cewar,
Daga bisani kuma, na samu ƙebewa da Shugaba Tinubun inda muka tattauna batun siyasar Kano da yadda jihar za ta ci gaba da zama lafiya.
Hakan na nuni da cewar da alamu maganar jita-jitar dake yawo na cewar Abba Gida-Gida da jagoransa Sanata Kwankwaso zasu iya komawa Jam'iyyar APC inhar shugaba Tinubu sai sanya baki wajen barmusu kujerar gwamnan Kano kenan.