Matukin adaidaita sahu yace bayan ya kammala sana'arsa ta wannan rana da misalin karfe 11:30 na dare, sai ya hangi wani buhu a cikin Babur dinnasa dauke da kayayyaki aciki.
Bayan ya bude yayi arba da magudan kudade ne kuma hankalinsa ya tashi cikin gaggawa ya juya Babur din nasa ya fita domin neman wannan mai kudi a cikin daren, sai dai bai samu wannan mai kudi ba, bayan yayatawa da yayi magana take ta gama gari, sai wasu bayin Allah suka gano wannan mai kudin.
Inda yace Babur dinma dayake hawa banasa bane shi sojan haya ne, bayan samun mai kudin shine yabashi tukwicin Naira Dubu 20, dalilin haka yasa yasamu karramawa daga wata kungiyar manyan sakatarorin Jihar Yobe.
Inda daga karshe kungiyar sukayi kira ga Gwamnatin Jihar wajen karrama wannan hazikin matashi.