Lamarin da ya faru a lokacin da "sojin na Najeriya suka yi yunƙurin kai farmaki kan ƴan bindiga," kamar yadda sojojin suka tabbatar.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a wata sanarwar da ya fitar a yau, Litinin.
Lamarin dai ya faru ne a daidai lokacin da wasu mutane suka taru domin gudanar da bikin Mauludi, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane "bisa kuskure" tare da jikkata wasu da dama.
"Gwamnatin jihar ta aike da manyan jami’anta don tantance halin da ake ciki, da bayar da tallafi ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma ba da shawara kan daukar matakan gaggawa don rage musu radadi.
"Ina tabbatar wa Æ´an jihata cewa har yanzu kariyarsu ce abin da muka fi bai wa fifiko a yakin da ake yi da ta’addanci da ‘yan fashi da masu aikata laifuka a jihar." in ji sanarwar
Wadanda suka samu raunukan za su samu kulawar gaggawa a asibitin koyarwa na Barau Dikko, inda gwamnati ta dauki nauyin kula da lafiyarsu.
Haka nan gwamna Sani ya yi kira da a kwantar da hankula tare da yin kira ga jama’a da su ci gaba da marawa jami’an tsaro da gwamnatin jihar baya a yakin da suke yi da masu aikata laifuka.