A wannan rana ta Alhamis ne majalisar dokokin Jihar Kano take saurararan shawarwari ga Al'ummar Jihar Kano kan kasafin kudi na shekarar 2024.
Kungiyoyi da dama da dai daikun mutane suka gabatar da bukatunsu domin majalisar ta duba ta kawo musu dauki a kasafin kudin shekarar dubu biyu da ashirin da hudu.
Wasu jama'ar da su sami damar zantawa da jaridar Raihana sun bayyana mata cewar idan da gwamnatoci zasu runga karbar shawarwari na kai tsaye ga al'ummar da suke wakilta da talaka bai kukan rashin adalci ba.