Rundunar yan sandan Jihar Kano ta cafke Daraktan Gudanarwa da Ayyuka na ma’ikatar ruwa ta jihar, Abubakar Gambo, tare da mataimakin sakataren gudanarwa, Baba Yahaya da kuma Nuhu Mansir,
Wanda tsohon manajan shirin noman rani a KAREFA ne a
Karamar Hukumar Tudun Wada, bisa zargin su da yin takardun bogi na samun izinin yi gwanjon wasu manyan injinan rarraba ruwan sha da kuma tankuna.
Ali Haruna Makoda wanda shi ne kwamishinan ma'aikatar ruwan sha ta jihar Kano, yace abinda wadannan mutane suka aikata ba da yawunsa su kayi ba, kuma tuni yan sanda na cigaba da bincike domin gurfanar dasu a gaban Shari'a.