A irin wannan rana ta shekarar 2022, kotun shari'ar musulunci karkashin jagorancin Malam Ibrahim Sarki Yola, ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, bisa wasu tuhume-tuhume guda hudu da ake masa.
Kwanaki 30 kotun ta bashi domin ya daukaka ƙara idan bai gamsu da hukuncin ba, bayan ta bada izinin rufe Masallatansa guda biyu, da kuma karɓe Littattafan karatunsa da umarnin kai su Babban Dakin karatu na gwamnatin Kano, tare da haramta sanya karatunsa a kafafen yaɗa labarai.
Tun a lokacin, Sheik Abduljabbar yace baya neman sassauci a wajen Alƙalin, illa a wajen Allah madaukin Sarki, don haka yana neman a gaggauta yanke zartar da hukuncin da aka yanke masa.