Barr Ibrahim (Matawallen Gwagwarwa) da farko ya mika godiyarsa ga Allah bisa cancanta daya bashi da jajircewa wanda har gwamnan Kano ya sahale masa da wakilci a karamar hukumar ta nasarawa,
A don haka yasha alwashin yin dukkannin mai yuyuwa wajen gannin ya fidda Gwamnatin Kano kunya.
A cewar Matawallen Gwagwarwa " Allah ya zabemu cikin miliyoyin al'umma dake karamar hukumar nasarawa, yankin dake da tsaffin gwamnoni da yantakarkarun gwamna da manyan yan siyasa da attajirai, malamai da dai sauransu mai girma gwamna da mataimakinsa suka zabemu damu mu shugabanci wadannan al'umma,
Kuma mu zama wakilai na Gwamnatin Kano, lallai wannan ba karamin abu bane a don haka bake tabbatarwa da Gwamnan Kano Alh. Abba Kabir Yusuf da Mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo dama daukacin shugabannin mu namazaba dana cafta lallai bazamu basu kunya ba cikin yardar Allah.
Ina kira da al'ummar karamar hukumar nasarawa da subamu hadin kai domin gannin munciyar da wannan yanki gaba, a karshe muna addu'ar Allah yabawa Gwamnan Kano da mataimakinsa nasara a kotun koli muna godiya kwarai da gaske"