Ana zargin ma’aikacin banki ya saci N3,390,000 daga asusun kwastoma a bakin United Bank Of Africa UBA dake Sharada a jihar kano
Jaridar Raihana ta rawaito cewa Garzali Wada Ibrahim yace ya kai ƙorafi bankin domin a seta masa manhajar da ake amfani da ita don tura kuɗi inda ya hadu da wani ma’aikacin banki mai suna Osaka Omada dake bangaren kula da kwastamomi wanda ya sake saita mushi manhaja ta wayar salula wato mobile application.
Ibrahim ya kara da Cewa a ranar 26 ga watan Nuwamba, 2023, an cire wasu kudade ba tare da izinin sa ba daga cikin Asusunsa har naira miliyan uku da dubu dari uku da casa'in (N 3,390,000) ta wannan manhaja dake wayar sa.
"Bayan an cire ne sai nayi mamaki kuma nayi zargin Osaka Omada na UBA din Sharada ne da yin wannan aika-aika domin babu wanda yaga lambobin sirrin cire kuɗi daga manhaja ta face Osaka domin yana kallo na saka." inji Garzali
Kashi na farko na kudaden da aka sata sun kai kimanin 2,000,000 inda aka tura su zuwa asusun bankin Wema mai lamba 7790847364 mai dauke da sunan BSTPOS-Musa.
Haka zalika kashi Na biyu na kudin da aka cire ya kai kimanin 1.300.000 inda aka tura shi zuwa asusun Opay mai lamba 9068129712 mai suna Angela Anulika weke
Ya kara da ceawa yayi yunkurin neman haƙƙin sa domin a dawo masa da kuɗaɗen sa amma haƙan sa yaci tura, saboda haka ya bukaci Babban Bankin Najeriya ya shiga tsakanin sa da Bakin United Bank Of Africa UBA rashen Sharada dake jihar kano.