Babban Sakataren jam'iyyar na kasa, Felix Morka, shi ne ya yi gargadin a wani taron manema labarai a yau Talata a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja.
Sa'o'i 48 da Yahaya Bello ya sauka daga mulkin jihar Kogi inda ya damka wa sabon gwamnan da aka zaba Usman Ododo, shafukan sada zumunta da muhawara sun cika da jita-jitar cewa Bellon na sha'awar kujerar shugabancin jam'iyyar.
A ranar Litinin an ga yadda hotunan tsohon gwamnan na Kogi suka yanyame titunan Abuja har da sakatariyar jam'iyyar da ke babban birnin Najeriyar.
To amma bayan taron babban kwamitin zartarwa na jam'iyyar, sakataren yada labaranta ya fito da sanarwa inda yake jaddada cewa a yanzu akwai wanda yake kan kujerar shugabancin jam'iyyar - wato tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Ya kara da cewa har yanzu Ganduje ne shugabansu saboda haka babu maganar takarar kujerar a yanzu kamar yadda magoya bayan Bello suke yadawa.
Ya ce kodayake wannan lokaci ne na dumukuradiyya to amma yana gargadin masu yada wadannan hotuna da su bari.
Saboda a cewarsa jam'iyyar na son mayar da hankali ne a kan yadda za ta daidaita al'amuran kasa a yanzu amma ba shugabancinta ba wanda ba su da matsala a kanshi.
Sai dai kuma tsohon gwamnan jihar ta Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya nesanta kansa da wannan kamfe da ke danganta shi da neman kujerar shugabancin APC.
Wata sanarwa da ofishin yada labarai na tsohon gwamnan ya fitar yau Talata ta zargi shugabannin hamayya da wadanda ya kira makiya a cikin jam'iyyar tasu da kitsa wannan abu domin bata sunan tsohon gwamnan.