Shugaban ɗariƙar kwankwasiyya tsohon gwamnan jihar kano Engr. Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa babu wata yarjejeniya ta fili ko ta ɓoye dake tsakanin su da shugaban ƙasar najeriya wadda ake zargin sunyi kafin yanke hukuncin kotun koli.
"Wasu da yawa na zargin cewa akwai yarjejeniyar siyasa tsakanin mu da Tinubu wadda mukai gabanin yanke hukuncin kotun koli amma ba haka al'amarin yake ba, amma dai na san cewa anja hankalin shi don kau da kai ga barin harkar shari'ar Najeriya ya kuma bari suyi abunda ya kamata'' inji Kwankwaso.