Wata sanarwa da CBN É—in ya fitar a ranar Alhamis, ya ce bankunan da aka naÉ—a shugabannin sun haÉ—a da Polaris, Keystone da kuma Union.
Sanarwar ta CBN ta ce an naÉ—a Lawal Mudathir Omokayode Akintola, a matsayin shugaban bankin Polaris, sai Hassan Imam, wanda ya zama sabon shugaban bankin Keystone.
Sai kuma Yetunde Oni a matsayin shugabar bankin Union.
NaÉ—a sabbin shugabannin na zuwa ne bayan rusa kwamitocin gudanarwar bankunan da CBN ya yi saboda karya dokoki da suka yi, ciki har da shiga ayyukan da suke barazana ga harkokin kuÉ—i.