A cewar gwamnan, majalisar za ta yi aiki a matsayin hukumar ba da shawara ga gwamnatin jihar .
Mai magana da yawun ABBA ya rawaito cewa mambobin majalisar sun hada da gwamnoni da mataimakansu da suka shude, shuwagabannin majalisar jiha da mataimakansu, shugaban majalisar dattawa da mataimakinsa (Idan akwai), alkalai masu ritaya, CJN mai ritaya (Idan akwai), Alkalan kotun koli da suka yi ritaya, alkalan kotun daukaka kara da Musulunci da suka yi ritaya. shugabanni, da sauransu.
Da wannan ne Rabiu Musa Kwankwaso, Ibrahim Shekarau, da Abdullahi Umar Ganduje ke zama mambobin majalisar.
Gwamnan ya jaddada kudirin sa na ci gaba da gudanar da gwamnati a bude domin tafiya da kowa da kowa.