Hukumar EFCC ta rike tsohuwar ministar ayyukan jinkai Sadiya Umar Farouk
A baya dai anyi zargin cewa tsohuwar ministar jin-ƙai a gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, Sadiya Umar Farouq ta miƙa kanta ga hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC domin amsa tambayoyi.
A saƙon da ta wallafa a shafinta na X, tsohuwar ministar ta ce ta amsa gayyatar da EFCC ta yi mata ne domin warware waɗansu batutuwa da hukumar yaƙi da rashawan ke bincike a kai.
A makon da ya gabata ne, EFCC ta gayyaci Sadiya Farouq domin neman bahasi game da zargin almundahanar biliyoyin naira da gwamnati ta ware domin yaƙi da talauci a Najeriya.
Da farko, tsohuwar ministar ta ce tana fama da rashin lafiya a don haka tana bukatar lokaci kafin ta bayyana gaban EFCC sai dai hukumar ta yi barazanar idan tsohuwar ministar ba ta bayyana cikin kwana uku ba, za ta sanya sunanta cikin waÉ—anda ake nema ruwa a jallo.