Da yake jawabi yayin bikin rantsar da sabbin manyan sakatarorin gwamnati da masu ba da shawara na musamman a gidan gwamnati, Gwamnan ya bayyana cewa babu wani farfaganda da zai hana gwamnatinsa cimma burinta.
Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa nadin shugaban ma’aikatan jihar a matsayin mukaddashin SSG ba yana nufin an kori Baffa Bichi daga mukamin sa ba ne .
Yayin da yake magana kan yada labaran karya, Abba Kabir ya bayyana cewa, wadanda suke dauki siyasa a matsayin madogararsu ta rayuwa, su ne suke kirkiro jita-jita don tada hankulan da ba dole ba, amma kuma hakan su bai cimma ruwa ba .
Gwamna Yusuf, yace na bada rikon mukamin sakataren gwamnati ne saboda muhimmacin da mukamin yake da shi, ba zai yiwu a tafiyar da gwamnati a haka ba.
Gwamnan ya bada tabbacin idan Baffa Bichi ya samu sauki, to da zarar ya dawo zai cigaba da aikinsa.