Kotun wacce ke dauke da kwamati mai alkalai guda biyar a gabanta, karkashin jagorancin Mai shari'a Inyang Okoro, yaki amincewa da sauraron karar da APC da hukumar zabe ta INEC daukaka daga bisani akan lamarin.
Zaman daya gudana a wannan rana ta Alhamis kwamatin Alkalan yasanar da Lauyan APC Wole Olanipekun (SAN) cewa babbar karar da aka shigar gabanta kotun ta hadesu bukatarsu wuri guda.
Adebutu da Jam'iyyar PDP sun nemi kotun kolin data kwace kujerar Gwamna maici na Jam'iyyar APC, inda suka dogara da hujjar kwace zabe na magudi da kuma rashin cancantarsa.
Anashi jawabin Lauyan Adebutu da Jam'iyyar PDP Chris Uche (SAN) yace kamata yayi hukumar zabe ta INEC ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe guda 99 da aka soke zaben su.
Haka kuma PDP da Adebutu suna neman kotun koli data soke hukuncin kotun daukaka kara datayi a ranar 23 Ga Watan Nuwambar shekarar data gabata ta 2023, daya tabbatar da hukuncin kotun sauraren kararrakin zabe data tabbatar da nasarar Adiodun a matsayin Gwamnan Jihar.
Dayake mayar da martani Lauyan INEC ya bukaci kotun koli data watsi da bukatar da Jam'iyyar PDP da Dantakarar ta Adebutu.
Bayan ji daga kowanne bangare Alkalan kotun Biyu sunyi watsi da bukatar Adebutu da Jam'iyyar PDP sakamakon rashin gamsassheyar hujja, sai dai Mai Shari'a Jane Esienanwan Inyang na gannin sabannin hakan, inda kotun ta nemi Hukumar zabe ta INEC data janye takardar shaidar cin zaben data bawa Abiodun na APC.