Matakin na zuwa ne bayan janye ƙarar da lauyan Mr Titus Uba na Jam'iyyar PDP, Sebastian Hon ya yi.
Titus Uba ya ƙalubalanci nasarar gwamna Hyacinth ne na jam'iyyar APC.
Sai dai kotun ƙararrakin zabe da ta ɗaukaka ƙara a Abuja sun tabbatar Alia ne halastaccen gwamnan jihar ta Benue bayan da hukumar aɓe INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce ba ta da hurumin sauraron ƙarar da aka shigar gabanta saboda batutuwan da aka yi ƙorafi a kansu sun faru ne gabanin zaɓen.
Kotun ta kuma ce kamata ya yi Uba ya maka mataimakin gwamna Sam Ode a babbar kotu bisa zargin mallakar takardar boge.
Ta kuma ce Uba ya gaza tabbatar da zarge-zargen da yake yi wa mataimakin gwamnan.